Jama'a wannan shine ake kira "awon igiya".


"Zamu ruguje gine ginen da akayi a cikin birnin jihar Kano,"


 "baza mu biya bashin da aka karba ba daga 18/3"


, zamu kori ma'aikatan da aka dauka ko aka canzawa gurin aiki".


Wai sabuwar gomnatin da ake tunanin zata temaki al'uma ce take wannan ikirarin.


A tunani na duk mai son cigaban jihar Kano idan yaji wannan shirmen, hankalin sa ne zai tashi, domin so ake a gina al'uma ba rusa ta ba.


Yau anyi gine gine masu kyau da ma'ana, inda yake maboyar masu laifi ya zama wajen neman abinci kuma Ya samu tsaro, gashi an kayata shi.


Inda yake tamkar daji yau ya zama gari, domin kuwa wajen da yake firgita mutane Ya zama wajen zama da neman abincin mutanen.


Idan ka dauki BUK Road abin gwanin sha'awa, masallacin Idi abin birgewa, domin duk guraren sun lalace amma yau sun zama abin sha'awa.


Bayan wannan al'uma yau suna acikin yanayi na neman dauki, ana tukawa da kyar amma kana maganar korar ma'aikatan da mafi yawan su matasane kuma magidanta, 


So akeyi a kirkirar mana 'yan ta'adda ko kuma almajirai ake son a Kara yawan su akan na bayan da ake son dakatarwa ?


Maganar bashi: duk gomnati tana tafiya ta bar bashi, so akeyi azo a damu mutane da zancen kotu ko kuma ayyuka za a tsaya ayi ko kuma dai kawai adawa za ayi ta tsayawa yi ?


Zamce ake na bunkasa ilmi, noma, kasuwanci, lafiya, tsaro, masana'antu da sufuri, bunkasa tattalin arziki, samar da aikinyi, inganta harkokin shari'a da tallafawa masu bukata ta musamman, etc.


Wadan nan sune abin dubawa kuma sune ake yiwa al'uma albishir akai, ta haka ne hankalin su zai kwanta su tabbatar ba a hannun 'yan awon igiya suke ba.


Allah Ya temake mu Yabamu dacewa duniya da lahira.


Muna masu bankwana da kyakkyawan tsari na Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da yi masa fatan alkhairan.

muryarhausaafrica.blogspot.com