DA ƊUMI-ƊUMINSA: Rashin sani Mutumin da aka ɗaka ɗawa dukan kawo wuma ba shi ya  sanar da zaɓen  Adamawa ba


Bincike kan wani faifan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta na soshiyal midiya in da ake yaɗa   cewa an cafke Kwamishinan zaɓe na Jihar Adamawa wanda aka yiwa dukan kawo wuƙa aka fasa bakinsa, aka kuma cire masa kayansa, ashe ba shi  ne ya sanar da zaɓen ba,  Farfesa A. A Zuru ne, tsohon VC na jami'ar Usman Danfodio University Sokoto wanda INEC ta  tura Adamawa a matsayin sa na mai sa ido kan zaben cike gurbi na Jihar.


Wasu ‘yan daba ne suka kai masa hari inda suka Lakaɗa masa dukan kawo wuƙa, domin sun ɗauka mwamishinan zaɓe (REC) Hudu Yunusa ne,  wanda ya ayyana Aishatu binani a matsayin wadda ta lashe zaɓe duk da ba'a kammala kawo wasu sakamakon ƙananan hukumomin goma cikin 20 ba.


Waɗannan ɓata garin sun ci zarafin wannan bawan Allah, sun keta masa rigar arziki akan abun da bai ji ba, bai gani ba, inda suka yi ta yayata hotunansa bayan su tuɓe masa kaya.